Ta Faru Ta Kare!: Rundunar Ƴan sanda ta hana goyo a babur a Kano

B9

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta fara aiwatar da cikakken haramcin ɗaukar fasinja a kan babura, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu kananan hukumomi.

Dokar, wacce gwamnatin jihar ta kafa a baya, tana shafar Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yanki na Jido) da Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido Ward).

Kwamishinan ‘Yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi masu babura da adaidaita sahu da su bi dokokin, inda ya ce duk wanda aka kama yana karya doka zai fuskanci hukunci.

Haka kuma, rundunar ta bukaci jama’a su kai rahotan  duk wani aiki na rashin tsaro ta hanyar layukan gaggawa na ‘yan sanda.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴansandan, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta bayyana cewa jami’an ‘yansanda da na KAROTA zasu tabbatar da abin dokar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *