Hukumar Shari’ah ta jihar Kano bayan ta musuluntar da Maryam da tayi ta kuma aurar da ita a ranar Alhamis ga wani matashi mai suna Muhammad Tukur daga Æ™aramar hukumar Bagwai.
Malam Ali Dan Abba wanda shine Kwamishina na biyu a hukumar kuma mai rike da hukumar a halin yanzu ne ya bada umarnin daura wannan auren a gaban Kwamishina na É—aya na hukumar Gwani Hadi da sauran daractoci da ma aikatan hukumar tare da wakilin shugaban Æ™aramar hukumar Bagwai Hon Engr. Bello Abdullahi Marafan Gadanya kuma kansila Hon. Engr. Mika’il Abdullahi Galawar Dutse
Da kuma iyayen ango da wanda ya zama wakilin amarya da sauran tawagar jama a da suka zo shaida wannan aure
Bayan daura auren Mal Ali Dan Abba ya ja hankalin ma’auratan kan zama lafiya da bin sunnar shugaba Sallallahu alaihi Wasallama, ya hori ango da ya kula sosai da sosai akan wannan nauyi da Allah ya dora masa, sannan kuma gashi wakilin Muslunci ne shi duba da musuluntar da tayi ga kuma aure.
Hakazalika ya ja hankalin iyayen angon kan sai sun taya shi angon wannan jahadi da yayi na taimakawa wajen musuluntarta sannan kuma ga aurenta da yayi.
A karshe kwamishinan ya godewa ciyaman din Bagwai Hon Engr. Bello Abdullahi Marafan Gadanya kan irin jajircewar da yayi a auren wajen yi mata kayan daki da kuma wasu kudade na alada da suka kai dubu dari da hamsin 350,000 na siyan dan akuya da lemo da girki duba da iyayen nata ba musulmi bane, kuma suka amince da wannan auren, Mal yace wannan bai yi mamaki ba duba da wannan tarbiyya ce ta mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir na jagora Engr Rabi’u Musa Kwankwaso.
Yayi kuma kira ga al’umma kan cewar akwai yara da hukumar tace rike da su wadanda suka musulunta iyayensu suka rabu da su ake basu tarbiyya mai kyau, da su zo su duba su aura domin kara musu kwarin guiwar zaman su cikin musulunci.
Shi kuma ango Muhammad Tukur Yau yayi godiya ga Allah a wannan rana ya kuma cewar bai taba tunanin zuwan wannan ranar ta haka ba domin ta dalilinsa Maryam ta karbi Musulunci kuma ga shi yau ta zama matarsa, alhamdulillah.
Ita ma Amarya Maryam Edo tace naji dadi da kasancewata a wannan rana kuma musulma kuma matar aure, babu abin da zan ce da Allah sai dai na kara gode masa.
A nasa bangaren wakilin ciyaman din Bagwai kuma kansila a wannan Æ™aramar hukumar Hon. Engr. Mika’il Abdullahi Galawar Dutse ya ce wannan aiki dama sun saba yin sa domin a wajen babansu Gwamna Abba Kabir Yusuf da kakansu Engr Rabi’u Musa Kwankwaso suka gada.
Sannan Engr Mika’il yayi kira ga sauran shuwagabannin kananan hukumomi da suyi koyi da nasu shugaban wajen yiwa addini hidima, domin tun da wannan lamari ya bijiro shugaban nasu yake ta fadi tashi na kokarin ganin ya shawo kan iyayen Maryam har aka sami nasarar aurar da ita a yau.







Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ