Duk Mai Hannu a Yankan Albashin Ma’aikata, Ya Kuka Da Kan Sa – Ina Ji ALGON

IMG 20250227 WA0045

Daga Aminu Bala Madobi

Biyo bayan korafe korafe na yankar albashin ma’aikata, Gwamnatin Kano ta sha alwashin daukar mataki cikin gaggawa a kokarin yiwa lamarin yankar albashin ma’aikata waigi.

A cikin wata sanarwa da Hajia Hon. Saā€™adatu Salisu Soja Shugabar karamar Hukumar Tudun Wada kuma Shugabar Shugabannin Kananan Hukumomi ALGON, tace daukar matakin ya zama wajibi don ceto ma’aikata daga wannan hali.

Kan wannan tankiya, Hajia Saadatu Soja ta bada tabbacin cewa, bayan taba-alli da da Gwamna Abba Kabir Yusuf, tuni aka kafa kwamiti don bincike dakuma yin Garambawul ga masu kokarin yin zagon kasa ga aikace aikacen Gwamnati.

“Al’ummar kano masu albarka, Bayan jin korafe korafen ku dakuma wanda na karanta da kaina kan matsalar yankar albashi, Ina tabbatar muku cewa mun taba-alli da Mai Girma Gwamna kuma tuni an kafa kwamitin bincike”

“Ina mai baku tabbaci zamu sa kafar-wando-daya da duk wanda ke da hannu cikin wannan lamari nan gaba kadan” Acewar ALGON

Rahotonni sun tabbatar da cewa ma’aikata a kano na kokawa gameda mas’alar yankan albashi wanda Gwamnati tace ba zata laminci duk wanda aka kama da hannu cikin wannan tirka tirka ba.

A ganawar Jaridar Alfijir da wasu ma’aikata sun koka cewa ana yanke musu albashi ba tareda wani dalili ba, wasu kuma ba sa ganin albashin ma kwata kwata.

Kan wannan lamari A wannan rana ta Alhamis Sakataren Gwamnatin kano ya jagoranci taron manema labarai domin aiwatar da tsare tsare a kwamitin da Gwamnati ta kafa cikin gaggawa don warware dukkan matsalolin dake tattare da barazanar albashin ma’aikata.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  šŸ‘‡

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group šŸ‘‡šŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *