Ta Sake Faruwa! Dan Jaridar ARTV Ya Bayyana Yadda SSR Din Gwamnatin Kano Ya Ci Zarafinsa A Bakin Aikinsa

IMG 155101 24226 1771944679169

Daya daga cikin Kwararrun masu daukar hoto a gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) Madi’u Adamu, ya bayyana yadda Auwal Sani Rogo, jami’in  gwamnatin jihar Kano, ya kai masa hari a bainar jama’a a lokacin bikin cika shekaru 65 da ‘yancin kai da aka gudanar a Kano.

Da yake magana kan lamarin, Mista Adamu ya yi zargin cewa rikicin ya faru ne yayin da yake gudanar da aikinsa na bikin cika shekaru 65 na ‘yancin kai da Najeriya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kofarmata.

“Ina yin aikina a matsayin mai daukar hoto ina daukar hotunan abubuwan da suka faru a bikin cika shekaru 65 na Najeriya kamar sauran ‘yan jarida da ke wurin, ba zato ba tsammani, Rogo ya kusance ni, ya tura ni kasa ya fara zagina a bainar jama’a a gaban jami’an gwamnati da sauran ‘yan jarida.”

Adamu ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin kunya da damuwa, musamman saboda ya faru a bainar jama’a a lokacin babban taron Kasa da gwamnatin Jihar Kano ta shirya.

“Abin takaicin ne kawai ina yin aikina na da Doka ta bani dama Rogo ya ci Zarafina, aka c mutunci na ban jiba ban gani ba, sai hakuri aka bani,” inji Madi’u.

Shaidu a wurin sun ce rikicin ya jawo hankali saboda yawan manyan mutane da ma’aikatan kafofin yada labarai da ke wurin.

“Ba wannan ne karo na farko da wani abu makamancin haka ya faru ba. A lokacin bikin ranar ‘yancin kai a filin wasa na Sani Abacha, ya kuma zage ni da kai hari a lokacin da nake aiki, duk lokacin da na tuna abin da ya faru sai na fusata nan take,” in ji Adamu.

Wannan lamari ya haifar da damuwa a tsakanin kafofin yada labarai a Kano, musamman bayan wani korafi da wani dan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai ya shigar a baya, wanda shi ma ake zargin Mista Rogo ya yi masa cin mutunci.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Mista Rogo bai fitar da wata sanarwa a bainar jama’a kan zargin ba. Gwamnatin Jihar Kano ba ta fitar da wani jawabi a hukumance kan lamarin ba.

Masu ruwa da tsaki a kafofin yada labarai sun ce lamarin ya nuna bukatar kwarewa da girmama juna tsakanin jami’an gwamnati da ‘yan jarida, musamman a lokacin tarurrukan da manema labarai suka yi.

Al’amarin yana ci gaba janyo muhawara yayin da kiraye-kiraye ke ƙaruwa don fayyace gaskiya da kuma warware matsalar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *