A safiyar Lahadin din nan ne wasu fusatattu Mutane mazauna Abuja suka kutsa kai cikin rumbun ajiyar kayan Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA) suka dakawa kayan wawaso saboda matsin rayuwa da ake fuskanta a fadin kasar.
Alfijir labarai ta rawaito mutanen sun kai harin ne a ma’ajiyar hukumar da ke Phase 3 na birnin tarayya Abuja.
Da take tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, in da ta ce, “Yanzu haka an samu nasarar shawo kan lamarin.
Idan baku manta ba irin abubuwan makamantan haka sun faru a Katsina, da hanyar Abuja zuwa Kaduna, in da aka tare motocin kayan abinci aka dakaru wasoso a kai.
Leadership Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V