Jami’an Hukumar (DSS) sun kama wani mutum mai suna Musa Abubakar, wanda ake zargi da kasancewa babban dillalin makamai da ke bai wa kungiyoyin da ke aikata hare-hare a Jihar Filato da wasu sassan Arewacin Najeriya.
An cafke shi ne a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, bayan samun sahihin bayanan leken asiri da suka kai ga gano wurinsa da kuma tsarin da yake amfani da shi wajen kerawa da kuma rarraba makamai.
Majiyar DSS ta shaida cewa, “Wanda ake zargin ya amsa cewa yana kera manyan makamai da harsasai tare da rarraba su ga kungiyoyin da ke gudanar da tashe-tashen hankula a Filato da Arewacin Najeriya.”
A yayin atisayen an gano kayan hada na’urorin fashewa (IED), sinadarai da kuma wasu na’urori da ake amfani da su wajen kera makamai, wadanda duk jami’an DSS suka kwace.
Wannan kamen na Musa Abubakar ya biyo bayan sake kama Abdulazeez Obadaki, wanda aka fi sani da Bomboy, wanda ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje, kuma ake zargi da shirya hare-haren Owo da Deeper Life Church.
A baya, hukumar ta kama mutunne 9 da ake zargi da hannu a hare-haren Filato da Benue, ciki har da Timna Manjol (46), wanda tun da farko ya amsa wasu daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da su, ciki har da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t