Ta’adanci! Yan Bindiga Sun Kashe Wani Malamin Jami’a A Ofishinsa Da Ke Maiduguri

FB IMG 1710620938451

Wasu da ba a san ko suwaye ba, sun yi wa malami a Sashen Nazarin Jiki da Lafiya na Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), Dr. Kamar Abdulkadir, kísan gílla a ofishinsa.

Alfijir labarai ta rawaito an káshe Abdulkadir ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da maharan suka kutsa cikin ofishinsa suka kai masa hari da wuka da guduma.

Majiyoyin leken asiri sun bayyana wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaƙi da tada ƙayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa, an ga gawar mamacin a cikin jini tare da rauni da dama a jikinsa. .

Maharan sun kuma tafi da motarsa da wasu kayayyaki masu daraja, amma an bayyana cewa, hukumomi na neman waɗanda suka aikata wannan mummunan lamarin.

Kazalika rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa, ta cafke mutane 8 da take zargi kan aikata wannan mummunan lamarin.

FB IMG 1712027074648
Marigayi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *