Ta’addanci! An Kama Wasu Matasa Kan Yi Wa ’Yar Shekara 13 Fyade A Gona

IMG 20240214 134342

Sun yi wa ’yar shekara 13 fyade a gona a garin Bajoga da ke Jihar Gombe

Alfijir labarai ta rawaito Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu matasa biyu da ake zargin su yi wa wata ’yar shekara 13 fyade a gona a garin Bajoga, Karamar hukumar Funakaye.

Kakakin rundunar, Mahid Mu’azu Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da matasan da wasu da ake zargi su 20 a a shalkwatar rundunar.

ASP Mahid ya kara da cewa matasan da ake zargin an kama su ne bayan rahoton da nahaifin yarinyar ya kai caji ofis, inda yake zargin sun yi wa ’yarsa fyade.

ya ce a ranar 8 ga watan Fabarairu ne mahafin ya kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke garin Bajoga cewa a ranar 7 ga wata matasan suka tare ’yar tasa a gona suka mata barazana, sannan suka yi mata fyade.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *