Yadda Aka Kama Wani Korarren Soja Dake Kai Wa Bello Turji Kayan Yaki

FB IMG 1707913490919

Ya fada a komar ’yan sanda a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’adda kayan sojoji a Zamfara daga Kaduna

Alfijir labarai ta rawaito yan sanda sun kama wani korarren soja da ke bai wa jagoran ’yan bindigan Jihar Zamfara, Bello Turji da yaransa kayan sojoji.

Korarren jami’in Sojan Saman Najeriyan mai suna Ahmed Mohammed, ya kasance yana samarwa da yan bindiga kakin sojoji na yaki da sauran kayan aikin jami’an tsaro, kafin dubunsa ta cika.

Aminiya ta gano cewa Ahmed ya yi aikin sojan sam kawai na tsawon shekaru biyar kafin a kore shi saboda wani laifin da ba a bayyana ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa, an cafke korarrren sojan ne tare da wani abokinsa a hanyarsu ta kai kayan jami’an tsaro da suka dauko daga Kaduna za su kai wani sansanin ’yan bindiga da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.

Adejobi ya ce Ahmed ne ya yi wa wani abokin nasa mai suna Mushiri Abubakar, tayin sayar wa ’yan bindiga da kayan da sojoji.

A cewarsa, Mushiri Abubakar ya samar wa sansanonin ’yan ta’adda daban-daban kayan sojoji bayan wadanda ake zargin sun bai wa Bello Turji da tawagarsa.

Da yake gabatar da su a hedikwatar rundunar da ke Abuja, Adejobi ya ce kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da kakin sojoji guda 10, da huluna da rigunan sanyi dai dai sauransu.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *