Ta’addanci! An Tarwatse Manyan Bututun Safarar Mai Na Gwamnatin Tarayya.

FB IMG 1742296318274

Daga Aminu Bala Madobi

Ana cikin halin dar-dar a yayin da wani abin fashewa ya tarwatse a manyan bututun samar da Man Fetur na Trans-Niger a Bodo, dake karamar hukumar Gokana ta jihar Ribas.

Fashewar ta faru ne a daren ranar Litinin a kusa da hanyar Bodo zuwa Bonny wadda ake ginawa.

Rahotonni sunce yankin da abin ya shafa na babban bututun mai a halin yanzu yana ci da wuta, ko da yake har yanzu ba a gano ainihin musabbabin dalilin fashewar ba.

Shaidar gani da ido sun tabbatarwa da Jaridar Alfijir cewa an hango wani bakin hayaki mai kauri ya turnuke sararin samaniya, inda wutar ta bazu cikin sauri daga wani faifan bidiyo da ya fito a safiyar Talata.

TNP wani Babban layin sufurin man fetur ne na gwamnatin tarayya da ke kai man fetur zuwa tashar fitar da kayayyaki ta Bonny dake jihar Ribas.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, jami’ai na ci gaba da gudanar da bincike kan ko fashewar na da alaÆ™a da ayyuka da mutane suka aikata, musamman duba da barazanar da kungiyoyin ‘yan bindiga suka yi a cibiyoyin man fetur a baya-bayan nan, lamarin da ya zamo a matsayin martani ga matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana kason jihar Ribas a cikin rudanin siyasa da ake ci gaba da yi tsakanin Gwamna Simi Fubara da Nyesom Wike.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *