Takaddama: APC ta bukaci Majalisar dokokin Ribas ta tsige Gwamna Fubara

IMG 20240507 WA0186

Daga Aminu Bala Madobi

Jam’iyyar APC ta umurci majalisar dokokin jihar Ribas, karkashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule, ya fara shirin tsige Gwamna Siminilayi Fubara nan take.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban kwamitin riko na jam’iyyar, Mista Tony Okocha, ya ba da umarnin a ranar Talata, yayin wani taron manema labarai a ofishinsa, a Fatakwal.

Umurnin ya biyo bayan sanarwar da gwamnan ya yi a baya-bayan nan cewa ‘yan Majalisar ba suda wani hallacci a idon doka.

Okocha ya bayyana cewa, idan majalisar ta kasa fara shirin tsige gwamnan, jam’iyyar za ta yi amfani da sassan da suka dace na kundin tsarin mulkin ta domin ladabtar da su a matsayinsu na ‘yan APC.

Idan dai ba a manta ba a ranar Litinin ne Fubara ya soki halin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas game da gwamnatinsa, inda ya ce ‘yan majalisar za su daina zama ‘yan majalisa idan ya ga dama.

Ya ce ‘yan majalisar na nan ne bisa amincewar sa da aka yi a kan yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.

Gwamna Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga tawagar shugabannin siyasa da na gargajiya daga jihar Bayelsa da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Fatakwal, babban birnin jihar, domin neman da kawo karshen rikicin siyasar jihar Ribas da kuma kyautata alaka a tsakanin jihohin biyu.

Ya ce, “Wadannan gungun mutanen da ke da’awar ‘yan Majalisa ba ’yan Majalisar ba ne, ba su da wani halacci a idon doka. Na yarda da waccan yarjejeniyar zaman lafiya don kawai a sami zaman lafiya. Gaskiyar kenan. Babu wani abu a cikin waccan yarjejeniyar zaman lafiya da ke da batun tsarin mulki; mafita ce kawai ta siyasa. Kuma na yarda da shi saboda wadannan mutane ne da suke cin abinci a gidana, wadannan mutane ne da na taimaka wajen biyan kudin makarantar ‘ya’yansu a lokacin ba ni ma gwamna. To, menene abin da ke can?

“Muna iya samun rarrabuwar mu amma na yi imanin cewa wata rana, mu ma za mu iya haduwa don ganin an samu zaman lafiya a jiharmu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *