Daga Aminu Bala Madobi
Wata mata mai suna Sarah Ayinde, ta bankawa mijinta wuta, Mai suna Abidemi Ayinde, jami’in ‘yan sandan jihar Ogun Dake zaune a unguwar Iperu da ke jihar Ogun.
Majiyar da ta nemi a sakaye sunan ta ta ce lamarin ya faru ne bayan da ma’auratan suka yi wata ‘yar takaddama.
Majiyar ta ce a ranar Lahadin da ta gabata ce 22 ga watan Disamba ne rigimar ta ta’azzara, inda matar ta kona dan sandan a wani yunkurin ramuwar gayya.
Majiyar ta ce, “Matar tasa ta kona wani karamin ofishin ‘yan sanda. Bayan wata takaddama da suka yi, sai matar ta banka masa wuta.
Yanzu haka mijin yana kwance a asibiti.” Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ta wayar tarho, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya bayyana cewa wanda abin ya shafa na kwance a asibiti, kuma tuni aka cafke wadda ake zargin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj