Takaitaccen Tarihin Marigayi Alh Bashir Usman Tofa

Takaitaccen Tarihin Marigayi Alh Bashir Usman Tofa

Best Seller Channel 

Best seller channel 

Best seller channel ta rawaito an haifi marigayi Alh Bashir Usman tofa a Kano a ranar 20, ga watan Yuni na shekara ta 1947. 

Yayi makarantar firamare ta Shahuci Junior primary school Kano, sai ya cigaba da karatu a makarantar City Senior Primary School a birnin Kano. 

Best Seller Channel 

Tsakanin shekara ta 1962-1966 ne , ya halarci makarantar Provincial College Kano. 

Bayan kammala karatu a wannan makarantar ne ya fara aiki da Royal Exchange Insurance tsakanin shekara ta 1967-1968. 

Daga shekara ta 1970 zuwa shekara ta 1973 ya je makarantar City London College. 

Tofa ya shiga harkar siyasa ne a shekara ta 1977 lokacin da yayi Kamsila a mazabar Dawakin Tofa.

 Daga bisani aka sake zabarsa a matsayin mamba a majalisar jaha. 

A jamhuriya ta biyu ne Bashir Tofa ya zama almajiran jam’iyyar NPN a jihar Kano har na wasu lokuta. 

Sannan kuma ya zama ma ajin kudi na Jam’iyyar. 

A jamhuriya ta uku kuma , Tofa ya hade da jam’iyyar NRC a shekara ta 1990. 

Best Seller Channel 

A shekarar 1993 lokacin Janar Badamasi Babangida yana shugabanin soja a Najeriya ne ya shirya tare da sabon tsarin OPTION A4, aka zabi Tofa a matsayin Dan takarar shugaban kasa, kuma ya kayar da Pere Ajunwa da Joe Nwodu da Dalhatu Sarki Tafida a zaben fidda gwani inda ya dauki tikitin yima jam’iyyar ta NRC takara. 

Tofa yayi rashin nasara a zaben hannun Moshood Kahimawo Olawole Abiola, daga yankin Yara awa a kasar. 

Amma daga baya Gwamnatin ta janar Babangida bata fidda sakamakon zaɓen ba.

 Tofa kuma ɗan kasuwa ne fitatacce a kasa da duniya baki daya. 

Kuma marigayin shine jagorancin INTERNATIONAL PETRO-ENERGY COMPANY (IPEC) da kuma ABBA OTHMAN AND SONS LTD. 

kuma ya zama mamba a kungiyar Century Merchant Bank and General Metal Products. 

Alh Bashir Tofa bai tsaya fannin kasuwanci ba kawai, shaharenren marubucin adabi ne, inda ya rubuta littattafan Ilmi daban daban don nazari a kai. 

Wasu daga cikin littattafan nasa sune:

1. Rayuwa Bayan Mutuwa

2. Tunaninka Kamanninka 

3. Musha Dariya 

4. Amarzadan Da Zoben Farsiyas

Da sauransu. 

Best Seller Channel 

Alh Bashir Tofa ya koma ga mahaliccinsa ne ranar Lahadi cikin dare a wani kaulin an ce ranar Litinin 3 ga junairu, 2022 bayan Gagariyar rashin lafiya da ya sha fama. 

An haife shi 1947 ya kuma rasu 2022 yana da shekara 75a duniya Kenan. 

Allah ya jaddada rahama, afuwa, gafara a gareshi, Allah ya bawa iyalansa da sauran masoya hakurin rashinsa ameen. 

Slide Up
x