Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Lahadi 11/02/2024CE – 01/08/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Tsohon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Access Holdings, Herbert Wigwe ya rasu a haɗarin jirgin sama a Amurka.

Har yanzu dai gwamnatin tarayya bata biya ma’aikata albashin watan January ba.

Hukumar alhazan Kano tace har yanzu bata sayar da kujeru sama da dubu 3 ba.

An kama mutum 32 da ake zargin su da yawon barace-barace a kan hanyoyin Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Rundunar ‘yan sandan Enugu ta kama wani boka da ake zargin yana amfani da dabbobi ba bisa ka’ida ba, da kuma yi musu kisan gilla da azabtar da su, da sunan tsafi.

Gwamnan Katsina Dikko Radda yace sunyi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai.

NDLEA ta kama mutum 92, muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 217 a Kaduna.

Akalla ciyamomi 3 ne a jihar Kano suka sauya sheka zuwa NNPP inda Gwamna Abba ya karbe su Kananan hukumomin sun hada da Dawakin Tofa da Garun-Malam da kuma Nassarawa da ke jihar.

Gwamnatin sojin Myanmar zata tilastawa ‘yan kasar karbar horon aikin soja.

Macky Sall ya ce a shirye yake ya sauka daga mulkin Senegal.

Sojin Amurka biyar sun mutu a hatsarin jirgin sama.

‘Yan ta’adda sun hallaka dakarun wanzar da tsaro na majalisar dinkin duniya a Congo.

Afrika ta Kudu ta lashe tagulla a Gasar cin kofin ƙasashen Afirka ne bayan doke DR Congo da ci 6-5 a bugun fenareti.

Asian Cup: Qatar ta lashe gasar kofin ƙasashen Nahiyar Asiya bayan doke Jordan da ci 3:1 a jiya.

EPL: Newcastle ta sami nasara akan Nottm Forest da ci 3:2 a wasan jiya.

Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan Girona da ci 4:0 a wasan jiya.

Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Roma da ci 4:2 a wasan jiya.

Bundesliga: Liverkusen ta sami nasara akan Bayern Munich da ci 3:0 a wasan jiya.

Lig 1: PSG ta sami nasara akan Lile da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *