Kuskuren Farko Da Tinubu Yayi Shi Ya Jefa Yan Najeriya A Wahala – In Ji Farfesa Itse Sagay

FB IMG 1707639417167

Itse ya soki gaggawan janye tallafin man fetur da aka yi a bara, kamata yayi sabon shugaban Najeriya ya jira sai matatun cikin gida sun fara aiki tukun kafin ya cire tallafi.

Alfijir labarai ta rawaito Tsohon shugaban PACAC, Farfesa Itse Sagay kuma babban lauya a Najeriya, ya soki tsarin janye tallafin man fetur da aka tabbatar da shi a 2023.

Hakan na kunshe ne Cikin wata zantawa da tashar Channels tayi da shi, Farfesa ya yi tir da da Bola Tinubu a kan daina biyan tallafin man fetur.

Sagay ya bada misali da matatar Aliko Dangote da ta gwamnati da ke Fatakwal, ya so ina ma sun fara aiki kafin fetur ya tashi. Itse Sagay bai ji dadin tashin fetur ba “Fetur yana da muhimmanci a rayuwarmu.

Tsadar rayuwa ta na ta karuwa kuma rayuwa tayi kunci. Ina tunani ya kamata a ce mun jira na watanni shida domin za a fara tace mai a gida, sai a cire tallafi. Gaggawa da yadda aka janye tallafin nan ta ke ya kirkiro wahalar da kusan da kyar ake rayuwa.

Sagay ya nuna rashin goyon bayan yadda ake tafiyar da abubuwa a yau, wanda ya sha bam-bam da gwamnatin da aka rantsar a bara.

Dole Shugaba Tinubu ya ceci Naira

A hirar da aka yi da shi, lauyan ya ce dole sai an yi hobbasa domin a ceci Naira wanda kullum ta ke kara rasa daraja a kan Dala. Ko a mafarki, Farfesan bai taba tunanin za a zo lokacin da za a canji Dalar Amurka a kan N1, 000, sai dai yana sa ran za a kawo gyara.

Gwamnatin Tinubu ta jawo tsadar fetur

A dalilin janye tallafi da gwamnati tayi, ana da labarin farashin litar man fetur ya tashi daga N190 zuwa kusan N700 a fadin kasar. Kwanaki an yi ta rade-radin fetur zai kara kudi, zancen da gwamnati ta karyata, ta kuma nuna ba a dawo da biyan tallafin man ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *