Tarin Nasarorin Da Muka Samu A Shekarar 2024 – In Ji Kwamandan Vigilante Na Kano

kwamandan Vigilante

Dsga Rabi’u Usman

Rundunar yan sintiri ta vigilantee a jihar kano ta bayyana yanda suka gudanar da aikace aikacen shekarar 2024 da muke bankwana da ita tare da bayyana shirin da sukayi na tunkarar shekarar 2025.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Babban kwamandan vigilantee na kano Alhaji Shehu Rabiu yayin zantawar sa da manema labarai yayin bankwana da shekarar 2024 da muke ciki.

Inda yace sun gudanar da manya manyan aikace aikacen da baza su manta da su ba musamman a shekarar da muke kokarin bankwana da ita domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano a sassan kananan hukumomin kano 44.

Aikace aikacen sun hadar da fatattaka da kama bata garin mutane masu haurawa gidajen jama’a, masu satar kayan Gona, masu kwacen wayoyin al’umma harma da masu garkuwa da mutane a wasu sassan kauyukan karkara.

Yana mai cewar, daga cikin nasarorin da suka samu a shekarar 2024 sun hadar da gudanar da aikin zaben kananan hukumomin kano 44 da ya wakana, tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma yayin zanga zangar tsadar rayuwa, tsaron rayuka yayin rikicin masarautar kano, dunkulewar vigilantee ta zama daya a jihar kano, Ginin katafariyar Babbar shalkwatar rundunar yan vigilantee da gwamnatin kano keyi a yanzu da dai sauran su.

Shehu Rabiu ya Sha alwashin jami’an vigilantee a jihar kano za su cigaba da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar ba dare ba rana domin tabbatar da inganta harkokin tsaro a fadin kano domin gudun kwararowar bata gari daga makobtan jihohin kano.

Yana mai nuna damuwar sa dangane da rasa rayukan wasu daga cikin yan vigilantee yayin da suke tsaka da aikin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kara da cewar, tuni suka shirya tunkarar shekarar 2025 da wasu sabbin dabarun aiki na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano musamman a loko da sakon unguwannin kano.

Kwamandan ya bukaci al’umma masu hannu da shuni ‘yan kasuwa da daidaikun jama’a dasu kasance masu taimakawa yan vigilantee da kayan aiki da biyan kudin hayar ofisoshin su harma da bayanan sirri da zarar sunga motsin abinda basu amince da shi ba domin kawo musu dauki na gaggawa.

Daga nan ya yabawa gwamnatin kano bisa yanda take basu gudummawa wajen inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *