Tinubu ya yi barazanar fitar da umarnin shugaban kasa kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi

FB IMG 1763928899556

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi barazanar cewa zai iya fitar da Umarnin Shugaban Ƙasa (Executive Order) domin a rika sakin kuɗaɗen rabon tarayya kai tsaye ga ƙananan hukumomi a faɗin Najeriya, idan gwamnonin jihohi suka ci gaba da ƙin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.

Tinubu ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Juma’a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC mai mulki, wanda aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban kasar ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu gwamnonin jihohi ke ci gaba da riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi, duk da hukuncin Kotun Ƙoli da ya ba su ’yancin cin gashin kansu ta fuskar kuɗi.

Tinubu ya jaddada cewa dole ne a aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli. Ya ce idan aka tilasta masa, zai ɗauki matakin fitar da umarnin Shugaban Ƙasa domin tabbatar da sakin kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomi.

A cewarsa, yana nuna fahimta ne kawai ga gwamnonin, amma ya gargade su cewa idan ba su fara aiwatar da hukuncin ba, sakamakon hakan zai bayyana a rabon kuɗaɗen tarayya na gaba (FAAC).
Wannan mataki na Shugaban Ƙasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan ’yancin kuɗi da ikon gudanarwa na ƙananan hukumomi a Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *