Shugaban kasa Bola Tinubu ya takaita Ministoci manya da ƙanana da Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya zuwa motoci uku kawai a ayarin motocin da suke amfani da su na aiki.
Babu karin motocin da za a basu don yin tafiye-tafiye.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
Acewar sanarwar, an sanar da wannan matakin rage kashe kudin ne a yau cikin wata sanarwa da Shugaban Kasa ya sanya wa hannu.
“A watan Janairu na wannan shekara, Shugaba Tinubu ya dauki matakai masu muhimmanci don rage kashe kudaden gwamnati, ta hanyar rage mutanen da ke tafiya tare da shi a kasashen waje daga 50 zuwa 20. A tafiye-tafiyen gida kuwa, ya rage su zuwa mutum 25.
“Haka kuma, ya rage mutanen da ke tafiya tare da Mataimakin Shugaban Kasa zuwa mutum biyar a tafiye-tafiyen kasashen waje da mutum 15 a tafiye-tafiyen gida.
A cikin umarnin da aka bayar a yau, Shugaba Tinubu ya kuma umurci dukkan ministoci, kananan ministocin da shugabannin hukumomi su samu jami’an tsaro biyar kawai da za a tura musu.
“Tawagar tsaron za ta kunshi ‘yan sanda guda hudu da jami’in Hukumar Tsaro ta DSS guda daya.”
Ya umurci cewa ba za a tura karin jami’an tsaro ba.
Shugaba Tinubu ya umarci Mai Ba shi Shawara Kan Tsaro na Kasa ya tuntubi Sojoji, da Jami’an Tsaro da na ‘yansanda domin tattauna yadda za a rage adadin motocin da ake amfani da su da kuma jami’an tsaron da ake tura musu.
“Dukkan wadanda abin ya shafa suna da wajibcin bin wadannan sabbin matakai nan take”.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj