Daga Aminu Bala Madobi
Wani lauya mai kare hakkin bil’adama, Hamza Nuhu Dantani Esq, ya caccaki dokar da Hukumar ‘yan sanda da Majalisar Dokoki ta kasa ta yi wanda ya bada damar tsawaita wa’adin Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun.
Dantani ya jaddada cewa tsawaita wa’adin Sufeton Yan Sandan na zuwa biyo bayan bukatar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na neman Egbetokun ya ci gaba da zama a kan karagar mulki har zuwa karshen 2027, Wanda hakan na iya haifar da illa ga tsaron kasa.
A cikin wani koke da ya gabatar a ranar Juma’a, Barista Dantani ya nuna damuwarsa kan matakin da majalisar dokokin kasar ta dauka, wanda ya ce ya kawo cikas ga tsarin shugabanci a rundunar ‘yan sanda, dakuma zagon kasa ga kundin tsarin mulkin kasar, da kuma zubar da mutuncin jama’a kan harkokin mulki.
Baya ga haka, Dantani ya koka da matakin da shugaban kasa ya dauka na tsawaita wa’adin Egbetokun a ofis.
Da yake bayar da misali da tanade-tanaden dokokin da ke jagorantar nadawa da kuma wa’adin Sufeton Yan sanda a Najeriya, Barista Dantani ya dage cewa tsawaita wa’adin Egbetokun na iya kawo rarrabuwar kai da hadin kan kasa.
Mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya yi tsokaci kan sashi na 7 da 18 (8) na dokar ‘yan sanda ta Shekarar 2020, wacce ta bayyana shekarun ritaya, wanda ‘yan majalisar tarayya suka sabinta tanadin dokar don karin wa’adin ga Egbetokun.
Gyaran dokar ‘yan sanda mai cike da cece-kuce da majalisar dokokin kasar ta yi ya sabawa tanadin doka, musamman daidaito a gaban doka, kamar yadda Barista Dantani ya gabatar.
“Babu wani jami’i da za a bar shi ya ci gaba da aiki bayan ya cika shekaru 60 na ritaya ko kuma shekara 35 na aikin fansho.
An haifi Mista Egbetokun ne a ranar 4 ga Satumba, 1964, kuma bisa kididdigar lissafi, ya cika shekaru 60, dole ya yi ritaya a watan Satumba 2024.
“Har ila yau, ba ya cikin tanadin doka (iii) da ke sama, domin shi ba jami’in shari’a ba ne, kuma ba malami ba ne, abin da ke tattare da abin da ya gabata shi ne, ta hanyar aiki da doka, IGP Egbetokun, wanda ya kai shekarun ritayar dole. 60, kamata ya yi ya yi ritaya.
Ya koka da yadda majalisar kasa ta rage karfin fadar shugaban kasa duk da cewa an raba madafun iko don yi wa dokar ‘yan sanda kwaskwarima saboda karin wa’adin da Egbetokun ya yi a ofis.
“Musamman, a ranar 23 ga Yuli, 2024, Majalisar Dokoki ta kasa karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas, sukayi gaggawar zartar da kudirin yi wa dokar ‘yan sanda ta 2020 kwaskwarima cikin gaggawa.
“Tun a ranar ne majalisar wakilai ta amince da dokar gyaran dokar ‘yan sanda domin ba wa ofishin IGP damar ci gaba da aiki har zuwa karshen wa’adin da aka tanadar a wasikar nadin nasa.
“A wannan rana, majalisar dattawan ma ta dauki matakin daya biyo bayan rokon da fadar shugaban kasa ta yi na a baiwa Kayode Egbetokun, IGP, dama ya ci gaba da yin wa’adinsa na shekaru hudu a ofis duk da cewa ya kai shekaru 60 na dole ya yi ritaya aranar 4 ga Satumba, 20204.
“Kudirin dokar ya nemi a gyara sashi na 18 na dokar ‘yan sanda ta 2020 domin baiwa jami’in da aka nada a matsayin IGP damar yin aiki fiye da kayyadaddun shekaru 35 na aiki ko kuma ya kai shekaru 60.
Mai fafutukar kare hakkin bil’adama ya bayyana matakin tsawaita wa’adin Sufeton a matsayin wanda bai kamata ba, kasancewar ya toshe ci gaban sauran kananan hafsoshin da ke kan gaba da zasu iya jagorantar kananan hafsoshi.
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya fifita cancanta fiye da dakile cigaban yansanda na kasa wajen nadawa da karin girma a rundunar ‘yan sanda.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ