Hukumar Yan sanda ta amince da ritayar manyan jami’an ‘yan sanda

IMG 20250131 210154

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta bayar da umarnin sallamar duk wasu manyan jami’an ‘yan sandan da suka haura shekaru 35 a bakin aiki ko kuma sun haura shekaru 60.

Matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan wa’adin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, wanda a kwanakin baya ya cika shekaru 60 a duniya.

Shugaban sashen hulda da jama’a na Hukumar Ikechukwu Ani, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce “Hukumar ta gabatar da muhimman taro na murabus din manyan jami’an ‘yan sanda da suka kwashe sama da shekaru 35 da kuma wadanda suka cika shekaru 60.”

Shugaban Hukumar, DIG Hashimu Argungu (rtd) ne ya jagoranci taron na musamman, wanda kuma ya samu halartar mai shari’a Adamu Paul Galumje, mai ritaya na kotun koli da kuma Hon. Kwamishinan da ke wakiltar ma’aikatar shari’a; DIG Taiwo Lakanu (rtd), Hon. Kwamishinan ‘yan sanda da ke wakiltar ‘yan sanda Cif Onyemuchi Nnamani, sakataren hukumar.

A cewar Ani, sauya matakin ya zama dole saboda sabani da dokar ma’aikata ta gwamnati mai lamba 020908 (i & ii), wacce ta tanadi yin ritaya bayan ya kai shekaru 35 na aiki ko kuma ya cika shekara 60.

“Hukumar ‘yan sanda a taronta na farko, ta amince da murabus na manyan jami’an ‘yan sanda da suka shafe fiye da shekaru 35 da kuma wadanda suka haura shekaru 60,” in ji Ani.

Egbetokun dai na ci gaba da fuskantar zazzafan cari tun a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu, lokacin da wani dan rajin kare hakkin dan Adam kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya amsa gayyatar ‘yan sanda a Abuja.

Daga baya ‘yan sanda sun tuhumi Sowore da laifin yin amfani da yanar gizo da kuma buga labaran karya akan Egbetokun a ranar Talata, 28 ga watan Janairu.

Laifukan, wanda aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, sun zargi Sowore da wallafa bayanai a shafin sa na X, inda aka ce ya kira Egbetokun a matsayin “ Haramtaccen Sufeton Yan Sanda.”

A cewar tuhume-tuhumen, ‘yan sandan sun zargi Sowore da yin kalamai masu zafi da ka iya ta-da zaune tsaye.

Sowore, a wani sabon sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, ya dage cewa wa’adin Sufeton Yan sanda ya kare.

Sai dai a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun ‘yan sandan Muyiwa Adejobi, a ranar Alhamis, Hukumar Yan sanda ta ce ikirarin Sowore ba shi da tushe balle makama.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana kallon ikirarin Sowore a matsayin wani yunƙuri na zubar da mutuncin jama’a da haifar da ruɗani game da shugabancin rundunar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *