Tsoffin daliban Federal Government College Kano (FGC) sun bayyana rashin jin daɗinsu kan wani shiri da ake zargin zai mayar da wani ɓangare na filin makarantar zuwa wurin kasuwanci. Daliban sun ce wannan mataki zai iya lalata tsarin koyarwa da kuma rage sararin da ɗalibai ke amfani da shi wajen karatu da wasanni.
A cikin koke da suka gabatar ga Bola Ahmed Tinubu, sun roƙi gwamnati da ta sake nazari kan wannan shiri tare da fifita muradun ilimi da jin daɗin ɗalibai. Sun jaddada cewa makarantar na da muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar matasa da gina ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani shirin gine-gine ne da zai sauya fasalin yankin zuwa tsarin gidaje ko kasuwanci, abin da ya ƙara tayar da hankalin al’umma. Sai dai har yanzu babu cikakken bayani daga hukumomin da abin ya shafa.
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira ga gwamnati da ta dakatar da duk wani mataki har sai an tattauna da bangarori daban-daban domin kauce wa matsala a gaba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t