Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya warware ƙarin girma har ninki biyu da ya yi wa dogarinsa, Nuruddeen Yusuf, biyo bayan caccaka da ya sha daga sassa daban-daban na ƙasar.
Tinubu ya ɗaga Laftanar Kanar Yusuf zuwa muƙamin Birgediya Janar, lamarin da ya janyo gunaguni da cece-ku-ce a tsakanin al’ummar ƙasar.
Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa wata majiya ta shaida mata cewa shugaban ya lashe aman nasa ne sakamakon ƙwararan hujjoji da aka gabatar masa.
Majiyar ta ce matakin soke wannan ƙarin girma ya zo ne bayan tattaunawa da manyan hafsoshin soji, da jami’an tsaro.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t