Tufka Da Warwara: RMAFC Ta Musanta Karin Albashi Ga Shugabanni

Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar Kula da Harakokin Haraji, Allocation da Fiscal Commission (RMAFC) ta musanta rahotannin kafafen yada labarai na cewa ta amince da karin albashin masu rike da mukaman siyasa da na shari’a da na gwamnati da kashi 114 cikin 100.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar RMAFC, Christian Nwachukwu ya bayyana hakan, in da ya kara da cewar shugaban kasa Bola Tinubu bai amince da karin albashin ma’aikatan gwamnati ba.

Kwamishiniyar tarayya a hukumar Rakiya Tanko-Ayuba ce ta bayyana karin albashin a lokacin da ta wakilci shugaban RMAFC, Mohammad Shehu, a wajen gabatar da rahoton kasafin kudin da aka duba ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a Birnin Kebbi. a ranar Talata 20 ga watan Yuni.

Sai dai ikirarin da kakakin hukumar ya musanta.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *