Daga Aminu Bala Madobi
Dan majalisar wakilai Adams Ekene ya mutu.
Ekene Adam, na jam’iyyar LP, na wakiltar mutanen Chikun-Da-Kajuru a majalisar tarayya daga jihar kaduna.
Wannan na zuwa ne sati guda bayan mutuwar Olaide Adewale Akinremi Dan majalisar wakilai mai wakiltar Ibadan ta Arewa.
Hakanan bayan sati guda aka sami rahotannin mutuwar Isa Dogonyaro, Dan majalisar tarayya dake wakiltar mutanen Garki da Babura a zauren majalisar wakilai ta kasa
