Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu.
Alfijir labarai ta ruwaito yayin da yake gabatar da kudirin mataimakin shugaban majalisar, kuma Wakilin kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa Mohd Bello Butu Butu ya ce, samar da masarautun zai taimaka wajen inganta aladun gargajiya na yankin da addinin musulunci da kuma warware sabani a tsakanin al ummarsu.
Da yake Karin haske akan kudirin dokar shugaban masu rinjaye na majalisar kuma Wakilin karamar Dala Alh. Lawan Hussain Chediyar’yan gurasa ya ce dokar ta baiwa gwamna damar nada wadanda suka cancanta a matsayin sarakunan masarautun, kuma sarakunan za su kasance karkashin ikon mai martaba sarkin kano.
Dokar Masautu masu daraja ta biyun sun hada da masarautar Rano da ta kunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da kuma Kibiya sai masarautar Gaya da ta kunshi kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu da masarautar Karaye da ta kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.
Shugaban Majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman Majalisar.
Da zarar gwamna Abba Kabir Yusuf ya saka hannu akan dokar kafa masarautun masu daraja ta biyu za ta fara aiki nan take.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj