Wani Jami’in Yan Sanda Mai Mukamin DPO Ya Rasa Ransa A Bakin Aiki

Alfijr ta rawaito Jami’in ‘yan sanda makamin DPO ya rasa ransa yana cikin barci.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da mutuwar Mojeed Adebayo Salami, jami’in ‘yan sanda mai kula da ofishin ‘yan sanda na kan iyaka ta Seme.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, a ranar Talata ya tabbatar da mutuwar Sufetan ‘yan sandan.

Hundeyin ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta wayar tarho cewa marigayin ya rasu ne da safiyar Talata.

Wata majiya mai tushe, wacce makusanci ne ga marigayi DPO, ta ce Salami ya yi barci ne da yammacin ranar Litinin kuma bai farka ba.

Hundeyin ya ce: “An tabbatar da mutuwarsa a wani asibiti da ba a bayyana ba a Badagry.

“An sanar da dangin marigayin mutuwarsa kuma an kai gawarsa Ede, Osun, garinsa, domin binne shi a matsayinsa na musulmi.”

An tura Salami ofishin ‘yan sanda na Seme a shekarar 2021, inda ya karbi ragamar mulki daga hannun P Casmen, Sufeto na ‘yan sanda.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *