Yanzu haka, matafiya dake kan hanyar zuwa Kano daga birnin Abuja sun makale a jihar Kaduna saboda cunkoson ababen hawa.
A cewar daya daga cikin matafiyan da ya bukaci a sakaye sunansa, motoci sun tsaya cak tun karfe 3 na daren jiya a kauyen Gwanin Gora wanda hakan ya tilasta musu kwana akan Titi.
Ya shaidawa Arewa Radio cewa har yanzu ba a san musabbabin cunkoson ba, amma yana zargin cewa wata mota ta Lallace ko kuma tayi hatsari.
Matafiyan sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike tare da daukar matakin gaggawa domin dawo da zirga-zirgar ababen hawa yadda ya kamata a titin na Kaduna zuwa Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇