Yadda Kasuwar Neman Miji Ko Mata Dake SHANGHAI, CHINA Ke Kaiwa Da Komowa

IMG 20240512 WA0165

Daga Aminu Bala Madobi

…Kuma ita wannan kasuwa tana ci aranakun asabar fa lahadi ne da misalin karfe 5 na yamma.

Bayan binciken da hukumar kidaya ta kasar sin tayi game da adadin maza marasa aure dake zaune a kasar ta China.

Alfijir Labarai ta rawaito Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin maza Milyan 24 dake zaune babu aure a kasar la’akari albarkar yawa da  buwayi gagara misali ya yiwa kasar.

kasuwar dai tana ci aranakun asabar da lahadi ne da karfe 5 na yadda inda samari da ‘yammata ke tuttuddowa zuwa wannan kasuwa domin neman abokiyar rayuwar aure.

A kasuwar in har ka shiga komi bakin jikin ka, ko kayi bandaro abune me sauki ka sami wanda kakeso ya tsindima kogin sonka wurjanjan ido rufe.

Wannan kasuwa, kasuwa ce kamar yadda kuka sani irin kasuwannin kantin kwari, kasuwar singa, kasuwar sabon gari, wadda jamaa ke dandazo, idan saurayi zai liqe hotan shi da sauran bayanan sa, haka ma idan mace ce, haka zata manne santalelen hoton ta da dukkan bayanan ta da ka iya jawo hankalin saurayin da yazo neman kalar wadda yake so.

A cikin bayanan masoyan da aka kai kasuwa, iyaye ko mutumin da ya kai kansa kasuwar ya kansa adadin shekarun sa, tsawon sa, sana’ar sa, abin da yake so da abinda yafi ye masa dadi a rayuwa, amma idan kana jin kunya,  ba sai ka sa hoton ka ba, bayanan ka kadai ya wadatar.

Mata da yawa kan kai kansu kasuwar domin neman ko da wani zai sunsuna a rabauta da samun hubbyn rayuwa.

Kasuwar maza bakake tafi kowacce samun tagomashi inda akanyi artabu dazarar an kyalla ido an hango santalelen bakin saurayi ko matashin dattijo da yaje wannan kasuwa domin neman abokiyar zama.

Iyayen yarinya kanyi hurwa tareda bin maza bakaken fata domin suyiwa allah suyiwa annabi su auri yarinyar su.

Bincike ya nuna cewa iyayen mataye ko mazajen da sukayi bandaro sukan je wannan kasuwa suyi bajakolin “yammata da samari awani kebabben guri wato (Park) ta inda kowa zai like hotunan wanda ya kawo kasuwar kuma in har ka jefa kafar ka cikin wannan kasuwa, tabbas ba zaka fito ba sai da zukekiyar matar aure ko kuma santalelen mijin aure wanda taku-tazo daya

KO YA AKE NEMO ABOKIN AURE

Ga dukkan mai neman abokin aure ko abokiyar rayuwa, ya kan je takanas cikin wannan kasuwar domin yin rijista ta hanyar mika hoto, da sauran bayanan rayuwar mutum da suka hada da adadin shekaru, abin akafi kauna ta hanyar cimaka da sauran su,
Kasuwar ta shahara a fadin kasar kuma ga dukkan alamu duk wanda ya shiga wannan kasuwa bai fitowa batare da yasami wadda yakeso ya aura ba.

WADANNE KALAR MAZA NE SUKA FI YIN KASUWA?

Kasuwar maza bakake ita kan gaba dake ci ganga-ganga wato mazaje launin bakar fata sunayin kasuwa sosai domin kuwa har daka musu wawa akeyi ko kuma a tafka artabu da zarar anyi ido hudu da irin su.

BABBAR TAMBAYA ANAN…

Shin a cikin abokan ka ko kawayenki wa zaku kai cikin wannan kasuwa?

IMG 20240512 WA0164
China
IMG 20240512 WA0166
china
IMG 20240512 WA0162 1
China

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *