Akalla mutane 42 ake kyautata zaton cewa sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da masu aikin Umrah a ƙasar Saudiyya.
Lamarin ya faru ne yayin da motar bus ɗin da ke ɗauke da masu ibadar ke kan hanyarsu daga Makka zuwa Madina.
Rahotanni sun nuna cewa motar bus ɗin ta yi karo da tankar motar Dizal, wanda ya sa motocin biyu suka kama da wuta, kuma yawancin fasinjojin da ke cikin motar ’yan ƙasar Indiya ne, musamman daga jihar Hyderabad.
Gwamnatin Kasar ta India a yanzu haka ta aike da tawaga Kasar Saudiyya domin ganin abinda ya faru.
Haka kuma kafin nan gwamnatin India ta kuma buɗe wani ofishin haɗin guiwa a Jeddah, domin samun sahihan bayanai daga hukumomin Saudiyya.
Hukumomi sun fitar da lambobin gaggawa da iyalai za su iya kira domin samun karin bayani, yayin da ake ci gaba da tabbatar da sunayen waɗanda suka mutu da wadanda suka jikkata. Rahotanni sun ce mutum ɗaya kacal aka tabbatar yana raye cikin fasinjojin.
Hukumomin Saudiyya sun fara bincike kan abin da ya haddasa wannan babban hatsari, musamman ganin cewa tankar Dizal ce ta taka rawa wajen ƙonewar bas ɗin.
Ana cigaba da jiran cikakkun bayanai da tabbatar da yawan mutanen da suka rasa rayukansu.
TST Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t