Wasu mahimman bayanan shugaba Tinubu kan cikar Najeriya shekaru 65 da ta samun ƴanci

FB IMG 1759304222912

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ƙasar ta samu gagarumin ci gaba tun bayan samun yancin kai a 1960.

Yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƙasar albarkacin cikar Najeriya shekara 65 da samun yancin kai, Shugaba Tinubu ya ce ƙasar ta samun ɓunkasa a fannin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da fannin ilimi.

”…dole ne a yaba wa ci gaban da ƙasarmu da samu. A yau Najeriya ta samu wadatuwar fannonin ilimi da kiwon lafiya fiye da lokacin da muka samu yancin kai”, in ji shi.

Shugaban na Najeriya ya ce a lokacin da ƙasar ta samu yancin kai a 1960, makarantun sakandire 120 ne a faɗin ƙasar, da ɗaliban da ba su wuce 130,000 ba.

‘”Amma bisa alƙaluman da muke da su a 2024, akwai makarantun sakandire fiye da 23,000 a ƙasarmu”, in ji.

Haka ma ya ce a lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai Jami’ar Ibadan da Kwalejin Fasaha da ke Yaba ne kawai manyan makarantu a ƙasar, amma bisa alƙaluman 2024 akwai jami’o’i 274 da kwalejojin fasaha 183 da kwalejojin ilimi 236 a faɗin ƙasar, yana mai cewa wannan adadi ya ƙunshi na gwamnatin tarayya da na jihohi da ma masu zaman kansu.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *