Wata Babbar Kotu Ta Aike Da ‘Yan Canji Biyu Zuwa Gidan Gyaran Hali A Kano

IMG 20240228 180914

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Nasir, ta yanke da wasu jami’an canji da ba bisa ka’ida ba Duke aikinsu hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne bisa samun su da laifin gudanar da canjin kudi ba tare da samun lasisi ba.

An daure masu laifin: da suka hada da Munkaila Sani da Mohammed Sani a gidan gyaran hali, bayan sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa EFCC shiyar Kano ce ta gurfanar da su a gaban kuliya.

Lauyar masu gabatar da Kara Aisha Tahir Habib ta roki kotun da ta yanke wa masu laifin hukunci dai dai da abun da suka aikata.

Lauyan wadanda ake kara, Abdulrahman Isah ya roki kotun da ta tausayawa wadanda yake karewa saboda tsofaffi ne kuma sun yi nadama kan abin da suka aikata.

Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin shekara daya a gidan gyaran hali da tarbiyya kowannen su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *