Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana shirin ta na gurfanar da Matasan nan su biyu a gaban kotu, bisa zarginsu da aikata laifin garkuwa da karamin yaro sannan suka hallaka shi bayan sun nemi kudin fansa.
Alfijir labarai ta rawaito kakakin yan sandan jahar SP Abdullah Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aike wa da manema labarai a birnin Kano a ranar Laraba.
Kiyawa, ya ce abun takaicin kuma mara dadin ji , da ya faru tun a Ranar 12 ga watan Fabarairu 2024 , inda ake zargin wani mai suna Isma’il Adamu mai shekaru 22 dake Unguwar Mariri , da hallaka wani Yaro mai suna Abdullahi Sani mai shekaru 14 a duniya.
Bayan jami’an yan sandan sun yi nasarar cafke shi ya bayyana musu cewar, sun aikata laifin ne da wani mai suna Ismail Rabi’u wanda akafi sani da Risi.
Tun daga wancan lokacin ne yan sanda suka shiga farautar Risi domin cafke shi kan zargin da ake Yi mu Su.
Binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa dukkan wadanda ake tuhumar sun amsa laifukansu , kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya hori jami’an yan sandan da su kara zage damtse wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, tare da shawartar jama’a a duk lokacin da suka ga wani abu da basu amince da shi ba, Su yi gaggawar sanarwar a ofishin Yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V