Wata Kwantena Ta Fado Kan Adaidaita Sahu Tayi Ajalin Dan Sanda Da Wata Mata

IMG 004642 24925 1758671222637

Wata babbar mota mai ɗauke da kwantena mai tsawon kafa 40 ta murkushe wani adaidaita Sahu a karkashin gadar Ijora Causeway a jihar Lagos, ranar Talata, inda wani jami’in ‘yan sanda da wata mata suka mutu nan take.

‎Rahotanni daga LASTMA sun nuna cewa hadarin ya faru ne yayin da direban motar mai rijista XP 368 AKD ke ƙoƙarin yin wani motsi mai haɗari, wanda ya yi sanadiyyar murkushe adaidita Sahu mai lamba KJA 364 QN.

‎Mutanen da suka tsira, ciki har da direban adaidita suhun, wasu sun sami raunuka a kafafunsu an kuma garzaya da su Asibitin domin basu kulawa ta gaggawa.

‎Wasu fusatattun matasa  sun yi ƙoƙarin kunna wuta a motar. Sai dai ‘yan sanda sun shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a wajen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *