Wata Sabuwa: Bello Turji Yayi Kakkausan Martani Ga Barr Bulama Bukarti.

Turji Da Bukama

Daga Aminu Bala Madobi

Bello Turji Kasurgumin dan ta’adda da ya addabi jihohin arewa maso yamma ya maida martani ga fitaccen masanin shari’a Bulama Bukarti kan kalaman fallasa da yayi cikin bayanan da ya wallafa.

Alfijir Labarai ta rawaito Bulama Bukarti yayi zargin cewa kasurgumin dan fashin dajin dake garkuwa da mutane ya kakabawa mutanen garin Moriki biyan harajin dole da yakai Naira milyan 50.

Cikin kunshin bayanan da Bukarti ya yi da shahararren dan jarida  mai binciken kwakwaf Bello Galadanchi sun ce babu wani dalili da zai sa dan bindigar ya kakaba haraji ga mutanen Moriki, shi da ba gwamnati ko wata hukuma dake karban haraji ba.

Sai dai a martanin da yayi cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna 5, Bello Turji ya tabbatar da ikirarin Bukarti na sanya biyan haraji ga mutanen Moriki kan asarar da suka yi musu.

“Tabbas maganar haraji da na sanyawa mutanen Moriki wannan gaskiya ne bai yi karya ba” Inji Turji

Sai dai Bello yayi bayanin cewa dalilin kakabawa mutanen Moriki wannan haraji bai rasa nasaba da irin barnan mutanen garin Morikin suka yima ‘yan uwansa na la’anta musu garken bisashe.

“Wallah ba mu yarda, mutanen moriki sun mana ta’asa, sun la’anta mana garken shanu samada 100, sun kashe mana ‘yan mata kanana biyu a birnin Yero”

“Sannan sun kashe mana mutane a watan 7 bayan zuwan su masallacin juma’a ba gaira ba dalili, tare kuma da kore mana garken Rakumi wanda yakai 1707 har izuwa yanzu babu su babu labarin su”

Cikin faifan bidiyon Bello Turji ya roki Shugaban hafsan hafsoshin sojoji Christopher Musa da ya baiwa wani Murtala Asada matsayin shugaban ‘yan banga.

“Ina rokon shugaban mu, Christopher Musa do Allah da ya baiwa Murtala Asada shugabancin kungiyar ‘yan banga”

Daga nan dan fashin dajin ya cigaba da cewa da yawa cikin bayanan da Bulama Bukarti yayi babu kamshin gaskiya ciki domin kuwa wanda ya bashi labarin, bai bashi gamsassun bayanai ba.

Bello Turji ya kausasa kalamai ga masanin shariar wanda ke fallasa irin tankiyar dake wakana ta dabaibaye jihohin arewa maso yammacin kasar nan da Turjin.

“Karnen yahudawa, Bulama Bukarti da Dan daudun nan wato Bello galadanchi suje subbincika irin ta’asar da akayi mana tukunna, muna rokon Allah yayi mana tsari da ire iren ku” Inji Bello Turji

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *