Daga Aminu Bala Madobi
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana fara yajin aikin ‘sai baba ta gani’ a jami’ar jihar Gombe (GSU) saboda gaza cimma matsaya a kan batun walwalar ma’aikata da yanayin aiki, kamar yadda shugaban ya bayyanawa manema labarai a ranar Laraba,
Alfijir Labarai ta rawaito shugaban kungiyar ASUU reshen GSU, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya ce shiga yajin aikin ya zama wajibi saboda tabarbarewar al’amuran koyo da koyarwa a jami’ar.
Shugaban ya bayyana cewa sun shafe shekaru da dama suna kokari tare da bin hanyoyin warware matsalolin ta hanyar tattaunawa amma abin ya ci tura.
“Daga cikin manyan dalilan shiga yajin aiki akwai batun gazawar gwamnatin jiha wajen aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ASUU a shekarar 2021 da bukatar neman kara yawan kudin da ake bawa jami’a da kuma biyan kudin alawus din koyarwa (EAA) na tsawon lokaci.
“Akwai wani bangare mai muhimmanci a yarjejeniyar da muka kulla da gwamnati a shekarar 2021, shine batun bawa jami’a kudin da yawansu ya kai miliyan N50 duk shekara, wanda har yanzu, bayan kusan shekara hudu har yanzu ko sisi basu taba bayarwa da sunan hakan ba,” a cewar Dakta Jauro.
Dakta Jauro ya kara da cewa rashin biyan Malaman jami’ar alawus din EAA na tsawon shekara biyar ya saka su a cikin mawuyacin hali tare da kassara kwazonsu na aiki.
Shugaban ya bayyana cewa rashin girmama yarjejeniyar daga bangaren gwamnati ya barsu da rashin wani zabi face su tsunduna yajin aiki tunda basu da wata sauran mafita.
WIKKI TIMES
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
Tinubu Yaya alkawari cewar ya kawar da ASUU strike Ina Kuma wannan sabuwa ta bullo….a yanayin da ake cikin bayan ya amince da living wages da let the poor Breath!!!