Wata Sabuwa! Isra’ila ta kai hare-hare Iran da Iraqi da Syria

Screenshot 20240419 093311 Facebook

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya bayar da rahoton fashe-fashe da aka samu a birnin Isfahan, a kusa da babban filin jirgin saman kasar. Haka kuma an ji fashewa a wasu wuraren a kasar ta Iran da Iraqi da kuma Syria.

Alfijir Labarai ta ruwaito akwai alamun da ke nuna cewa hare-haren ramuwar gayya ne na Isra’ila, kan harin da Iran din ta kai mata kwana shida baya.

Daman duk tsawon mako ana ta hasashe a kan lokaci da kuma yadda Isra’ila za ta mayar da martani kan harin ba-zata da ba a taba gani ba wanda Iran ta kai mata- harin da ya fito yakin fakaice da dadaddun abokan gabar biyu ke yi a tsakaninsu fili.

A yanzu kafar yada labaran Iran ta ruwaito cewa an ji karar fashe-fashe a kusa da wani sansanin soji a birnin Isfahan, lamarin da ya sa aka dana garkuwar kariya ta sama ta birnin da ma sauran birane na kasar ta Iran.

Hotunan bidiyo da aka sanya a shafukan intanet sun nuna yadda ake ta harba makamai masu linzami na kare Iran ta sama.

Wani mai karnta labarai a tashar talabijin ta kasar, ya bayar da labarin fashewar:

Ya ce, kafofin labarai sun ruwaito cewa an ji karar fashewa mai girma a lardin Isfahan. Zuwa yanzu ba akai ga sanar da dalilin karar ba. Hukumomin yankin sun ce suna gudanar da bincike a kan lamarin.

Rahotanni sun ce an dakatar da zirga zirgar jiragen sama a biranen Iran da dama.

A ranar Asabar da daddare ne dai Iran ta harba wa Isra’ila makamai masu linzami da jirage marassa matuka na sama 300.

Da taimakon kawayen Isra’ilar an yi nasarar kakkabe da damansu kafin su kai ga Isra’ilar.

Jamian Israilar sun nuna cewa za su kai hari Iran din domin ramuwar gayya da kuma taka mata birki.

Shugabannin duniya suna ta kira ga Israilar da ta kai zuciya nesa a martanin nata don gudun kada lamarin ya fantsama a yankin na gabas ta tsakiya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa yankin na Gabas ta tsakiya na cikin wani yanayi mai matukar hadari.

Iran ta ce ba ta yi asarar komai ba sakamakon fashewar.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *