Wata Sabuwa: Kwamishinan Sufuri Yayi Murabus Sakamakon Belin Kasurgumin Dilan Kwayoyi.

FB IMG 1754463981196

Daga Aminu Bala Madobi

…Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala ya ajiye mukaminsa na Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano a ranar Laraba.

Dalilan Ajiye Muƙamin:

Kwamishinan Sufuri Hon Ibrahim Namadi ya bayyana cewa muradin jama’ar kano da kuma girmama gaskiya da amana ne suka sa ya yanke wannan shawara.

Yace ko da yake bashida wani laifi, sai dai cece kucen yayi yawane kuma ba zai iya watsi da yadda jama’a ke kallon lamarin ba, musamman bayan bincike kan batun bayar da beli ga wanda ake zargi da safarar ƙwayoyi.

Yace wannan mataki yana da muhimmanci don kare martabar gwamnatin da ya yi aiki a ciki.

Jawabinsa:

> “Kamar yadda muke a cikin gwamnatin da ke yaki da fataucin da shan miyagun ƙwayoyi, dole ne in ɗauki wannan mataki — koda yake yana da zafi.”

Martanin Gwamnati:

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin tare da fatan alheri ga Hon. Namadi a gaba. Ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan gaskiya da adalci don farantawa kanawa wadanda suka zabe shi

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *