Wata Sabuwa! Zakanya Ta Tsere Ta Shiga Gari

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Afrika ta Kudu ta gargaɗi al’ummar wani yanki bayan da wata zakanya ya tsere daga cikin wata mota da ake tafiya da ita a lardin Arewa maso Yammacin Ƙasar.

An ce zakanyar ta tsere ne a lokacin da mai ita ya ɗauke ta a bayan wata babbar mota.

Ba a bayyana ainihin lokaci ko yadda zakanyar ta tsere daga cikin motar ba, sai da mai ita ya isa inda zai je a garin Tlakgameng, sannan ya gane ta tsere, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

A yanzu ma’aikatan gandun daji da manoma na aikin farautar zakanyar.

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci duk wanda ya ga zakin da ya kai rahoto ga hukumomin kula da muhalli.

Hakan na zuwa ne bayan da wasu Damisa biyu suka tsere a watan da ya gabata a lardin Gauteng.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *