Garba Musa Kwankwaso, ƙanin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shigar da kara a gaban kotu kan ta hana gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar daukar wani mataki a kan wani fili.
A cikin karar har da hukumar KNUPDA da Kwamishinan Shari’a na jiha da sauran wasu mutane.
DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa asalin filin kwa Kwankwaso ne ga baiwa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai gwamna Abdullahi Ganduje ya kwace.
Daga baya sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jiha ga tabbatar da kwace filin, wanda ya ke a unguwar Kwankwasiyya City., bisa hujjar cewa lokacin da su ka bada filin WAECO bai yi rijista a cikakken kamfani ba.
Daga nan ne sai Ganduje ya dawo da kasuwar yan magani cikin wani bangare na filin.
Shi ma Abba da ya hau, sai ya ƙi maidawa kamfanin WAECO filin, shine Garba Kwankwaso ya shigar da kara.
A umarnin da ya bayar, Mai Shari’a Usman Na’abba ya bada umarnin hana taba filin ga gwamnati sannan ya dage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwamba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj