Wata Sabuwar! Matukin Jirgin Sama Ya Mutu Ana Tsaka Da Sheka Gudu A Samaniya

Airline

Wani matukin jirgin saman Turkish Airlines ya mutu bayan ya yi rashin lafiya a jirginsa da ya taso daga Seattle da ke gabar tekun arewa maso yammacin Amurka zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun ce direban Jirgin mai suna Ilcehin Pehlivan, dan shekara 59 ya mutu ne yana tsaka da tuka Jirgin wanda hakan yasa sauran direbobin Jirgin suka yi gaggawar sauka a filin Jirgin Sama na JFK da ke birnin New York a Amurka.

Jirgin ya sauka a birnin New York kimanin sa’o’i takwas da tashi daga Seattle.

Mista Pehlivan dai ya yi tafiya da kamfanin jiragen saman Turkiyya ne tun a shekarar 2007, kuma an yi masa gwajin lafiya akai-akai a farkon watan Maris, wanda bai gano wata matsalar lafiya da ka iya shafar aikinsa ba, in ji kamfanin.

Kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Turkiyya TATCA ta ce ya shafe shekaru da dama yana yi wa al’ummar sufurin jiragen sama hidima tare da mika ta’aziyya ga iyalansa da abokansa da abokan aikinsa.

Kawo yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar matukin jirgin ba. Dole ne matukan jirgi su yi gwajin lafiya a duk bayan watanni 12, yayin da wadanda suka haura 40 ke sabunta takardar shaidar lafiyarsu duk bayan wata shida.

Channels

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *