’Yan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisar jihar Ogun, Moruf Musa, a Ibiade da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside ta jihar ranar Talata.
Musa, wanda ya taɓa zama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa daga shekarar 2007 zuwa 2011, an rawaito cewa an kama shi da misalin ƙarfe 7:00 na yamma yayin da yake gudanar da sallah a cikin masallacin da ke cikin gidansa.
Shugaban ƙaramar hukumar, Ganiyu Odunoiki, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya ce an sace shi ne a lokacin sallar Magariba, kuma ’yan bindigar sun harba bindiga a kan hanya yayin da suke guduwa da shi.
Odunoiki ya ce, “Rahoton gaskiya ne, an sace tsohon ɗan majalisar a daren Talata. ’Yan bindigar ma sun harbi wasu mutane a kan hanyarsu ta guduwa.”
Ya ƙara da cewa: “Yanzu haka muna bincike a dazukan da ke kewaye da yankin tare da ’yan sanda, duk da cewa muna jiran rundunar yaki da sace-sace, wadda take kan hanyarta don haɗa kai da mu. Kwamandan yankin na ’yan sanda daga Ogbere ma yana nan.”
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, DSP Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da sacewar.
Ya ce rundunar ta san da lamarin kuma ta ɗauki matakan tsaro don tabbatar da dawowar Musa gida lafiya.
Babaseyi ya ce: “Rundunar ’yan sandan jihar Ogun ta san da rahoton sace Hon. Musa Moruf a Ibiade, ƙaramar hukumar Ogun Waterside. An ɗauki matakan tsaro, ciki har da tura rundunar yaki da sace-sace, kuma jama’a su kwantar da hankalinsu har sai an fitar da sanarwar hukuma.”
Wata majiya a kusa da gidan ta ce sai da tsohon ɗan majalisar ya yi taƙaddama da masu garkuwar na kusan tsawon mintuna 20, lamarin da ya jawo hankalin mazauna yankin.
Majiyar ta ƙara da cewa ’yan bindigar sun yi harbi a sama don tsoratar da mutane kafin su gudu da shi.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t