Wata Sabuwar! Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – In Ji Akintoye

FB IMG 1736250716263

Shugaban Ƙungiyar Ƙudirin samar da  ‘Yancin Kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba.

A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60  ciki har da mazauna gida da ‘yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Da ya ke tattaunawa da jaridar The PUNCH a jiya Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Najeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala.

“Ba kwa jin muryar mu a tituna? Ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya.

“Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Najeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsayin Najeriya, babu matsala,” in ji shi.

Daily Nigerian Hausa

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *