Ya Kamata Gwamnati ta Samar da hukumar da Zata Rika lura da Kafafen Sada Zumunta – Sanusi Bature

ptroz

“Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta san muhimmancinku domin yanzu zamani ne da ake tafiyar da komai ta yanar gizo, don haka dole ne mu karfafe ku mu baku duk gudunnawar da kuke bukatar domin inganta aiyukan ku”.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin ci gaba da kyautata kyakykyawar Alakar dake tsakanin ta kafafen yada labarai dake yada labarai ta yanar gizo.

Kwamishinan yada labarai na jihar kano Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani da kungiyar Kafafen yada labarai ta yanar gizo ta shiryawa ya’yanta da sauran abokan aiko a kano Yau alhamis.

Yace kafafen yada labaran yanar gizo suna taka muhimmiyar rawa wajen yada labaran da suka shafi aiyukan gwamnatin jihar tare kuma da kokarin fitar da labarai na gaskiya musamman a kafafen sada zumunta saboda yadda labaran karya sukai yawa.

” Mun San kuna da kwarewa, saboda kun je makarantar an koya muku, kuma hakan ya baku damar bayyanawa duniya labarai na gaskiya sabanin yadda yan social media suke yada Labarai ba tare da la’akari da tantance gaskiyar labarin ba”. Inji Baba Dantiye

A nasa jawabin mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bukaci gwamnatin tarayya data samar da wata hukuma da zata rika lura da aiyukan kafafen yada labaran dake aiki yanar gizo da ma kafafen sada zumunta.

Yace yin hakan zai taimaka wajen magance yada labaran karya da suke yin yawa a kafafen sada zumunta, wadanda yace suna haifar da ruɗani sosai a cikin al’umma.

A jawabinsa shugaban kungiyar kafafen yada labaran dake aiki a yanar gizo wato Association of Online Media Guild (ASSOMEG) Abdullatif Abubakar Jos ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda take baiwa yan jaridu hadin kai, sannan ya bukaci gwamnatin data daina dauka kiyayyace take sawa yan jaridu suke yin labarin da ya sabawa ra’ayoyinsu.

” Dole ne yan jaridu su zamo suna bibiyar aiyukan hukumomin gwamnati domin tabbatar da cewa gwamnatin tana yiwa al’umma aiyukan da suke bukata, sannan kuma hakan zai taimakawa gwamnatin ta yiwa al’ummarta aiyukan da suka dace domin inganta rayuwar su.

A yayin taron an gabatar da makaloli guda biyu, kan yadda yan jaridu zasu rika yin binciken kwa-kwaf da kuma yadda zasu banbance labaran karya a kafafen sada zumunta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *