Yadda Aka Gudanar Da Shagalin Bikin Aure Mai Cike Ta’ajibi A Kano.

IMG 20240730 WA1609

Daga Aminu Bala Madobi

Kamar yadda aka saba a duk lokacin bikin shagali, akan ci a sha, sannan asha shagali ta hanyar gayyato mawaka don yin raye-raye a gwangwaje da sunan murnar.

Sai dai a wannan biki kallo ne ya koma sama a yayin wasu ma’aurata suka tsayar da komai a gabar da suka shigo dandalin shagalin cikin wata shiga ba kamar yadda aka saba ganin Amarya da Ango nayi a wannan zamani ba.

Wakilin jaridar Alfijir ya bayyana cewar amaryar da matashin angon sun fito, wajen shagalin bikin sanye da dogon Hijabi, Nikab da kuma safar hannu da ta  Kafa in da ta rufe dukkanin ilahirin jikinta ruf a lokacin da ake tsaka da gudanar da murnar bikinta.

A yayin da Amarya ta fito cikin wannan shiga nan ta ke mai kula da kayan sauti DJ ya yi hanzari ya kunna wani take irin na kasar Larabawa wanda ya yi daidai da irin wannan shiga ta kasaita ta Amarya.

Sai dai duk da haka amarya ko gezau bata yi ba na shaawar takawa a salon sautin da ya kunna musu  wanda yayi daidai irin shigar larabawa da ta yi.

Wannan lamari ya zowa wasu daga cikin al’umma da mamaki sakamakon yadda ake ganin wasu Amare a yayin gudanar da shagalin bikinsu, ke sanya kaya mai bayyana tsiraici da surar jikin su da sunan murna amma sam hakan ba abu ne mai kyau ba.

Shin ko zaku iya kwatanta irin wannan salo a lokacin bukukuwan ku??? Muna jiran sakonninku.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *