Daga Auwalu Tahamu Zarewa
A jiya Alhamis, manoma sun kawo amfanin gona da yawa a Kasuwar Hatsi ta Giwa, wanda ya jawo yawaitar kaya a kasuwa.
Sai dai kuma, cikin ikon Allah, an samu yawan masu saye, lamarin da ya taimaka wajen tafiyar da ciniki sosai.
A hasashe, da ace ba a samu masu saye ba, da farashin kayan gona ya ƙara karyewa sosai. Amma kasancewar ciniki ya yi kyau, kasuwa ta ɗan daidaita.
GA YADDA FARASHIN YA KASANCE:
Farar dawa — ₦32,000 zuwa ₦35,000
Dawa kaura — ₦31,000 zuwa ₦33,000
Jar dawa (Janjare) — ₦43,000 zuwa ₦44,000
Barkono dan miyere — ₦30,000 zuwa ₦33,000
Barkono dan zagade — ₦27,000 zuwa ₦30,000
Shinkafa tsaba — ₦95,000 zuwa ₦112,000
Shinkafa tuwo — ₦95,000 zuwa ₦110,000
Shinkafa samfarera — ₦33,000 zuwa ₦40,000
Farar masara — ₦27,500 zuwa ₦29,000
Jar masara — ₦28,000 zuwa ₦29,000
Masarar gugguru — ₦55,000 zuwa ₦63,000
Dauro — ₦42,000 zuwa ₦45,000
Gero — ₦42,000 zuwa ₦44,000
Alkama — ₦50,000 zuwa ₦82,000
Busasshen rogo — ₦23,000 zuwa ₦26,000
Farin wake mai bakin hanci — ₦80,000 zuwa ₦85,000
Jan wake — ₦85,000 zuwa ₦94,000
Farin wake dan Misira — ₦78,000 zuwa ₦83,000
Farin wake dan Giwa (Zafa) — ₦78,000 zuwa ₦83,000
Farin wake dan Amarya — ₦83,000 zuwa ₦86,000
Farin wake kanana (Alale/Kosai) — ₦104,000 zuwa ₦106,000
Farin wake na farashi — ₦74,000 zuwa ₦77,000
Waken suya — ₦67,000 zuwa ₦69,000
Kamfala beans (Honey beans) — ₦87,000 zuwa ₦90,000
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t