Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin hutu a fadin kasar

FB IMG 1765280873650

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin hutu domin bai wa ma’aikata damar bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati, ta cikin wata sanarwa da babbar sakatariya ta ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a Abuja.

Ministan ya yaba da kokarin ma’aikatan Najeriya wajen ci gaban kasa, yana mai cewa gudunmawarsu na da matukar muhimmanci ga bunkasar tattalin arziki da walwalar al’umma.

Ya kuma bukaci ma’aikata su rungumi kishin kasa, aiki tukuru da sadaukarwa, yana jaddada cewa wadannan halaye na da muhimmanci wajen samun ci gaba mai dorewa.

Hakazalika, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kula da jin dadin ma’aikata da tsaron su, tare da samar da yanayi mai kyau ga ci gaban tattalin arziki.

A karshe, ya taya ma’aikata murnar gudanar da bikin ranar 1 ga Mayu cikin lumana, tare da kira gare su da su yi amfani da ranar wajen tunawa da muhimmancin hadin kai da aiki tukuru wajen gina kasa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *