Yadda Hisbah ta kama wata mata da ta mayar da gidanta wajen baɗala da tarin wasu mata a Kano

Screenshot 20240502 141404 Samsung Internet

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wata mata da ake zargin ta mayar da gidan da ta karba haya amma ta maida shi wajen saukar baki , maza da mata su na aikata baɗala.

Alfijir labarai ta rawaito mukaddashin babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dakta Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta aike wa manema labarai a yau Lahadi.

Ya ce an kama matar a unguwar Samegu bayan mazauna unguwar sun kawo korafin ta’adar da ta ke yi.

Hakazalika hisba ta kama wasu ‘yan mata a titin filin sukuwa da ake zargin ana daukar su ana kai su Otel domin yin lalata da su. Ya kuma kara da cewa  jami’an Hisbah sun kama har da masu juna biyu da masu goyo a cikin matan.

“A ci gaba da ayyukan hukumar Hisbah na tsaftace jihar kano daga aikata badala cikin yardar allah yau hukumar ta kai sumame unguwar titin filin sukuwa inda wasu yara ‘yan mata suke aikata badala,  ana daukarsu ana kaisu hotel ana lalata dasu.

“A cikin su har da masu ciki da masu goyo, haka kuma an cafke wata mata data maida gidanta mafakar badala inda take basu hayar dakinta a unguwar Samegu an kamata da maza 3 mata 3 haka,  ana yn  bincike a kanta dan gano mutanan da suka bata hayar gidan”,  inji Sanarwar.

Ya ce kamen wani ci gaba ne na ‘Operation Kauda Baɗala’ da runudnar ke yi don gyaran tarbiyya a jihar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *