Jaridar Alfijir labarai ta rawaito cewa, a kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyi, Hukumomi da masana tsaro sun yi kira ga jama’a da su sanya ido kan abubuwan da kan je yazo la’akari tsanantar matsalar tsaro.
Cikin wasu bayanai, hukumomin sun imanin cewa bin tsari tare da kai rahoto ga hukumomin gwamnati mafi kusa abune muhimmi da ke taka rawa don tabbatar tsaron lafiya da dukiyoyi.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun tabarbarewar tsaro kan al’amura da dama ke cigaba da kamari da suka hadar laifukan garkuwa da mutane, sace sace, fyade, cin zarafi, da wulakanta dan adam.
Don sauÆ™aÆ™e bayar da rahoto, hukumomin tsaro daban-daban sun ba da mahimman lambobin waya. WaÉ—annan layukan wayoyi don ba da damar mika bayanai ko rahotanni cikin gaggawa ta hanyar sadarwa kai tsaye tare da jami’an tsaro, don tabbatar da saurin mayar da martani ga kowacce irin barazanar da ke iya faruwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumomin tsaron sunce ya zama wajibi mai kira ko tura sakon neman agajin gaggawa ya kasance yana dauke da bayanan hujja a rubuce ko ta hanyar hotunan don zama shaida, kuma kar a yi jinkirin tuntuɓar hukumomin da abin ya shafa.
A cewar su mataki na gaggawa zai iya hana cutar da wani ta hanyar kare rayuka da dukiyoyi.
Don saukakawa, ga mahimman lambobin waya don kiyaye su:
– Laifukan Fyade: 08072732255
– Layin Kar-ta-kwana na Taimakon Yan Mata: 08072732255
– Layukan Taimakon Cin Zarafin Yara: 08085753932, 08102678442
– Rikicin Gida na Manya: 08102678443, 08057542266
– Rikicin Cikin Gida na Yara: 08107572829, 08131643208
Sauran lambobin waya masu muhimmanci don bibiya, lura da sa’ido sun haÉ—a da:
– Rundunar Sojojin Najeriya Masu Kula da ‘Yancin Fan adam NAHR: 08160134303, 08161507644
– Lambar Neman Agajin Gaggawa: 070-55350249, 070-35068242, 080-79279349
– Motar asibiti: 112, 199
– Layin Kai Rahoton Kokarin Kashe-Kai-Da-Kai: 08062106493, 08092106493, 09080217555, 09034400009, 08111909909, 07013811143
Tsarin tuntuÉ“ar ‘Yan Sanda da Tsaro
Idan akwai wani bayanai da ya shafi bangaren yan sanda cikin gaggawa, a tuntuɓi:
– Lambobin Gaggawa na ‘yan sanda: 01-4931260, 01-4978899
– Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP): 08059666666 (Sako kawai)
– Hukumar tsaron farin kaya SSS ta jiha: 08132222105–9
– Layukan Taimako na DSS : 08101272302, 08025713190, 08176878575, 09058530351
– Hukumar kiyaye haddura ta tarayya FRSC: 122, 07002255372
Alfijir labarai ta rawaito a lokacin bayar da rahoton ayyukan dake faruwa, ya zama wajibi a bada fifiko wajan bada cikakken adireshi da bayanai wanda zasu kasance abin dogaro ayayin bibiya. Kuma ya kasance ayi komi a sarari lokacin da ake tuntuɓar hukumomin, sannan kuma a dora mahimman bayanai a shafukan sada zumunta.
Hukumomin sun ce ta hanyar yin taka tsantsan da ba da rahoton ayyukan dake wakana ne kawai za a ba da gudummawa ga tsaro na al’ummominmu.
Mu tabbata mun tura wannan bayanai ga yan uwa da abokan arziki domin su amfana, mu yi aiki tare don samar da yanayi mai aminci ga kowa da kowa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj