Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jinjina kyautar mota SUV da Kwankwaso ya ba shi a kakar babban zaben 2015, Buhari yace motar sulken da tsohon gwamnan Kano ya ba shi kyauta ta taimaka masa a harin bam din Kawo A shekarar 2014 da ake shirye-shiryen zabe, an kaiwa Buhari harin bam a kasuwar Kawo dake birnin Kaduna.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake tabo zancen farmakin da aka kai masa a jihar Kaduna, shekara daya kafin babban zaben da ya lallasa Goodluck Jonathan.
Shugaba Buhari ya tsallake rijiya ba tare da samun rauni ba a tashin
bam ɗin wanda ya auku a kasuwar Kawo dake birnin Kaduna, hadimansa uku suka jikkata aka hanzarta kai su Asibiti.
A wancan lokacin, hadimin shugaba Buhari ya ce dan kunar bakin waken da ya kai harin wanda ya tuƙo Motar Toyota Sienna, ya kutsa cikin ayarin Buhari sannan ya tashi bam din.
The Cable tace Duk da shugaban ƙasan ya tsallake harin amma a Motar da yake ciki Toyota Land Cruiser da wata dake bayanta sun yi kaca-kaca sanadin harin.
“Abubuwa masu mahimmanci game da Muhammdu Buhari,” shugaban ƙasan ya ce motar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba shi ta taimaka masa ya tsira daga harin.
Daily Trust ta rahoto Buhari na cewa:
“Kwankwaso mutum ne mai karamci da hangen nesa, shi ya bani kyautar motar
sulke Land Rover. Ya gaya mun na yi amfani da ita domin tseren da na shiga ya kunshi masu son ganin baya na.”
“Na fito zan tafi Kano daga Kaduna a cikin wannan motar kwatsam wata mota
ta kutso zata wuce amma Dogarai na suka dakatar da su, ba zato suka tashi Bam.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Assalam alaikum. To Alhamdu da wannan sheds Da Shugaba Buhari yayi wa Kwankoso, To Tambaya a na shine , Shiko Buhari Wane Temano ko gudumuwa ko wane Alhairi ta taba yiwa Senator Kwankoso tun yayin da ya samu mulkin Nigeria har say biyu. Ko kuma yanzu kafin ya sauka me zai Yi was Kwankoso. Don saka Alhairi da aikin Alhairi. Ashe ba zai ce da Yan Nigeria ki zabi Rabi u Musa Kwankoso shine zai iya Zama Shugaba Mafi facewa da adalci a gareku Yan Nigeria ba ?
Idan wannan ba me zai Yi masa Nan gaba don nuna hallaci ko?
Allah ya kara kauna
Ameen ameen
Allah ne ya tsare ka Ba Mota Baba
Daga baya kenan , anyi sadaka da karuwa , tunda baihaka nuna masa halinkaba