Alfijr ta rawaito Gobara da ta tashi da safiyar Litinin a kan Titin Airport Road da ke birnin Kano, ta kone wasu shaguna da ake gudanar da harkokin kasuwanci, gobarar ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa.
Gobarar ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiya a kusa da makarantar GSS Stadium da ke kan titin.
Wani shaidan ganau ya bayyana cewar, wutar NEPA ce ta haddasa faruwar lamarin a wani shagon siyar da kayan mota, da wanda ake siyar da kayan Asibiti da ragowar Shagunan.
Kakakin hukumar kashe Gobara na jahar Kano PFS Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa tashin Gobarar ya faru ne a kusa makarantar sakandire ta GSS Stadium, da har yanzu ba su kai ga tantance musabbabin faruwar ba.
Saminu ya kara da cewa wutar ta faro ne daga wani shagon siyar da kayan Asibiti sannan ta tsallaka zuwa wasu shagunan da ake siyar da kayan Mota da na saida kayan Bandaki.
Ya kara da cewa, har yanzu ba su kai ga tantance yawan dukiyar da aka yi asarar ta ba, sai sun tuntubi mamallaka wajen sannan za su iya sanin dukiya da aka yi asara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Allah ya mai da alkairi